Kotu ta umurci tsohon Gwamnan Zamfara Matawalle ya dawo da motocin gidan gwamnati

Babbar kotu da ke zamanta a Sokoto ta yi watsi da bukatar tsohon Gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle kan hakkin mallakar motocin gidan gwamnati da ya tafi da su bayan ya sauka daga Gwamna a watan Mayun, 2023.

A watan Juni, 'yan sanda sun shiga gidajen Matawalle suka kwaso motocin da ke ciki kamar yadda kotu ta umurta.

A cikin wata sanarwa daga mai magana da yawun Gwamnan jihar Zamfara Sulaiman Bala Idris ya sanar cewa kotu ta yi watsi da bukatar Matawalle a kan wadannan motoci.

Sulaiman Bala Idris ya ce tsohon Gwamnan na jihar Zamfara wanda yanzu haka shi ne karamin ministan tsaro a Nijeriya, shi da wasu jiga-jigan gwamnatinsa, sun kwashi motocin da aka ware wa ofisoshinsu suka bar gwamnatin Dauda Lawan babu motocin da za su yi amfani da su.

Sanarwar ta tunaso cewa duk a cikin watan Juni, gwamnatin Dauda ta ba Matawalle da saura mukarrabansa wa'adin kwanaki biyar na su maido da wadannan motoci. Ya ce bayan kin bin wannan urni ne ya sa gwamnati ta nemi iznin kotu ta je ta kwaso wadannan motoci.

Bayanai sun ce a baya, akwai kotun da ke zama a Gusau babban birnin jihar Zamfara, ta umurci da a maida wa Matawalle motocin, inda Matawalle ya sake shigar da wata kara yake neman kotun ta halasta masa wadannan motoci.

A haka ne, gwamnatin Dauda ta nemi a mayar da shari'ar a babbar kotu.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp