Hukumar dake yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya
na bukatar gwamnatin tarayya ta kara yawan kudaden da aka ware mata daga naira
biliyan 43 zuwa naira biliyan 76 a cikin kasafin kudin badi.
Wannan bukata na kunshe ne cikin wata takarda da
shugaban hukumar Ola Olukoyede ya mikawa kwamitin kudi na majalisar wakilan
kasa.
Takardar na kunshe
da bayanin bukatar siyawa hukumar sabbin motoci na akalla naira biliyan 2 da
miliyan 600 sai wasu karin naira biliyan 33 da hukumar ke son ayi mata.
Da fari dai an warewa hukumar naira biliyan 37 da gudanar da
ayyukan yau da kullum da kuma naira biliyan 4.7 don cike gibi idan bukatar
hakan ta taso da kuma naira biliyan 1.2 don gudanar da manyan ayyuka.
Jaridar Premium
times ta ruwaito tun kafin shugaban kasa ya gabatarwa majalisar kasafin kudin
badin hukumar ta EFCC ta gabatar masa da wannan kuduri nata, sai dai kuma
shugaban bai shigar da bukatar ba, saboda wani dalili nasa.
Da yake kara yiwa ‘yan majalisar jawabi kan bukatar kara yawan
kudin, Mr Olu yace akwai bukatar a wadata hukumar da kudi gudun kada rashin
kudade isassu a hannu ya sanya ta fada karbar cin hanci a maimakon yaki da shi.