Kungiyar kare hakkin dan adam ta Amnesty International ta ce adadin wadanda harin bam din sojoji ya kashe a kauyen Tungar biri na jihar Kaduna ya kai 120 zuwa yanzu.
Bayanai na nuna cewa har yanzu babu wani alamu a
aikace na daukar mataki kan sojojin da suka aikata wannan danyen aiki, in banda
Allah wadai da gwamnati ta yi.
Har ya zuwa yanzu dai akwai mutane fiye da 50 da ke
kwance rai a hannun Allah a asibiti suna karbar kulawar jami’an lafiya bayan
wannan abin takaici da ya rutsa da su.
Sai dai kuma adadin da Amnesty ta bayar ya ci karo
da wanda hukumar bayar da agaji ta kasa NEMA ta bayar wanda ke cewa kawo yanzu
mutane 85 ne suka mutu a sanadin harin, yayin da 66 suka jikkata.
Wannan dai ba shi ne karon farko da jami’an sojoji
ke hallaka mutane da sunan kuskure a arewacin Najeriya ba, inda kididdiga ke
nuna cewa ire-iren wadannan hare-hare sun kashe mutanen da basu ji ba basu gani
ba har sama da 400 daga 2014 zuwa yanzu, musamman a jihohin Borno da Zamfara.