Majalisar wakilai ta umarci jami'an tsaro su kama gwamnan babban bankin kasa





 Majalisar wakilan Najeriya ta baiwa jami’an tsaro umarnin kama gwamnan babban banki CBN Mr Olayemi Cardoso da Akanta Janar ta kasar Mrs Oluwatoyin Madein da karin wasu mutane 17, sakamakon kin amsa gayyatar da ta yi musu a lokuta da dama.

Wannan umarni na zuwa ne bayan bukatar hakan da dan majalisa Fred Agbedi daga jihar Bayelsa ya mikawa majalisar.

Da yake karantowa majalisar muhimmanci kamo mutanen, ya ce dabi’ar su ta kin girmama majalisar ya nuna irin girman kan da suke da shi da kuma raina majalisa.

Don haka ne ya ce ya zama dole majalisar ta yi amfani da karfin da take da shi wajen tursasa musu gurfana a gaban ta, dalili kenan da ya sa kakakin majalisar Tajudden Abbas ya umarci babban sufeton ‘yan sanda na kasa da ya kamo mutanen da kuma tabbatar sun duka a gaban majalisar.

Majalisar na bukatar su gurfana gaban ta don yi mata bayani filla-filla kan abinda zasu yi da kudaden da aka ware musu a cikin kasafin kudin badi.

Post a Comment

Previous Post Next Post