Gwamnan Kano ya umurci Abdullahi Musa ya kula da ofishin SSG

https://drive.google.com/uc?export=view&id=1h4mmNfT8qSDNpAxGvJn4ZN2wlsxmP6t8

Gwamnan Kano Enge Abba Kabir Yusuf ya umurci shugaban ma’aikatan gwamnatin jihar Abdullahi Musa ya kula da ofishin sakataren gwamnatin jihar. Bayanan da DCL Hausa ta tattaro daga majiyoyi a gwamnatin ta Kano sun ce Abdullahi Musa zai kula da ofishin kafin sakataren gwamnati Abdullahi Baffa Bichi ya samu koshin lafiya. Sai dai Majiyar Ta DCL ta ce hakan ba ya nufin cewa an sauke sakataren gwamnatin jihar ta Kano.


Post a Comment

Previous Post Next Post