Kungiyar kasashen yammacin Africa ta ECOWAS ta zargi sojojin da suka yi juyin mulki a kasashen Nijar, Mali da Burkina Faso a matsayin wadanda ke rura wutar ta’addanci a nahiyar
Shugaban majalisar
gudanarwar kungiyar Omar Tourey ne ya bayyana hakan lokacin da yake jawabi
wajen bikin bude taron kungiyar kan tsaro da shiga tsakanin rikice-rikice karo
na 51 da aka fara a Abuja.
Tourey ya ce juyin mulkin
da sojojin suka yi, ya rusa duk wani tsari ko kokari da kungiyar ke yi na
tabbatar da tsaro a yankin.
Ya kuma kara da cewa jan
kafar da sojojin ke yi wajen mika mulki hannun farar hula na baiwa ‘yan ta’adda
da masu daukar nauyin su kara azama wajen kaddamar da hare-hare kan fararen
hula.
Tourey ya kuma nuna
takaicin sa kan yadda sojojin ke amfani da juyin mulkin wajen yada farfaganda
irin ta siyasa yayin da suke nunawa duniya cewa zaluntar su ake yi.
Kididdiga ta nuna cewa juyin mulkin da
sojoji suka yi a wadannan kasashe ya jefa jama’a kusan miliyan 5 cikin yunwa da
bakin talauci, sai wasu miliyan 2.5 da suka rasa muhallan su, inda ya tilasta
rufe makarantu fiye da dubu 9.