Za'a ci gaba da amfani da tsaffin kudi har sai baba ta gani-Kotun Koli


Kotun Koli ta bayar da umarnin ci gaba da amfani da tsaffin takardun Naira kafada-da Kafada da tsaffin har sai baba ta gani, ma’ana babu wata rana da aka sanya da za’a daina amfani da tsaffin kudi.

Kotun ta ce a yanzu bata amince a sanya wata rana da za’a daina amfani da kudaden ba, har sai lokacin da gwamnatin tarayya ta samar da sabbin dubarun sauyawa tsaffin kudin fasali ko kuma amfani da sabbi kadai, bayan taba alli da masu tuwa da tsaki kuma kotun ta amince da tsarin, wanda dole ya kasance ba zai cutar da ‘yan kasa ba.

Kotun mai alkalai shida karkashin jagorancin mai shari’a Iyang Okoro ta yanke wannan hukunci ne bayan da gwamnatin tarayya ta mika mata bukatar kara lokacin da za’a ci gaba da amfani da tsaffin kudade.

Gwamnatin tarayyar dai ta mika wannan bukata ne, bayan da ta ce ba zata iya buga sabbin kudaden da zasu wadaci ‘yan kasa kafin nan da ranar 3 ga watan Maris da mai zuwa ba, kamar yadda kotun ta tsayar a baya ba.

 

Post a Comment

Previous Post Next Post