Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya gabatar da kasafin
kudin badi a gaban zauren majalisun dokokin kasa da safiyar yau, inda adadin
kudin ya zarce naira triliyan 27.
Kasafin kudin ya kunshi
ciyo bashin akalla naira triliyan 7.8, yayin da aka yi hasashen sauyin kudin
dala akan naira 700 zuwa 750, inda kuma aka ajiye farashin kowacce gangar mai
kan dala 73, wanda za’a rika fitar da akalla ganga miliyan 1.78 kowacce rana.
Yayin gabatar da jawabin sa, Mr Tinubu ya ce majalisar
zartaswa ta sanya tsaron cikin gida da kuma na kan iyakoki kan gaba yayin tsara
wannan kasafi, don haka suna cikin bangarorin da zasu tafi da kaso mai tsoka.
Haka kuma kasafin ya sanya ci gaba dan adam musamman
kananan yara akan gaba, yayin da ya yiwa jami’o’i da sauran manyan makarantu
albishirin samun tagomashi a cikin kasafin.
Shugaban kasar Tinubu ya
ce ana sanya ran tattalin arzikin kasar nan zai habbaka da kaso 3.76 cikin 100,
la’akari da yadda tattalin arzikin duniya ke tafiya a halin yanzu, yayin da ake
sa ran tashin farashin kayayyaki zai dai-daita kan kaso 21.4 a badin.
Zamu kawo muku yadda rabon
kasafin ya kasance, a dakace mu.