Sabuwar Zanga-zanga ta barke a Kano

 


Sabuwar zanga-zanga ta barke a jihar Kano, yayin da jama’a ke ci gaba da nuna fushin su kan hukunci kotun daukaka kara da ta ayyana Nasiru Yusuf Gawuna a matsayin wanda ya lashe zaben bana, a maimakon Abba Kabir Yusuf da hukumar zabe ta INEC ta sanar.

 

Wannan ba ita ce zanga-zanga ta farko da al’umma a jihar ke gudanarwa ba, cikin makonni biyu da suka wuce, yayin da suke ganin shari’ar na cike da kura-kurai musamman bayan bullar takardun kotu da ke nuna cewa Abba Kabir Yusuf ne ya yi nasara ba Nasiru Gawuna ba.

 

Duk da kotun daukaka karar ta fitar da sanrwar da ke nuna cewa hukuncin ta na nan daram, kuskure ne aka samu a takardun, amma hakan bai hana jama’ar Kano nuna shakku da kuma bayyana fushin su ta hanyar zanga-zanga ba.

 

A wani labarin na daban duk a jihar Kano na cewa al’ummar Unguwar Kurna da Rijiyar Lemo a karamar hukumar Dala, sun rufe hanyoyi tare da kone-konen tayoyi da kuma zanga-zanga don nuna fushin su game da zargin wani dan sanda da harbin matashin dan wasa na kungiyar kwallon kafa ta Kurna Samba Alhaji Salisu Rabi’u tare da karin wasu mutane biyu.

 

Har yanzu babu wani martani game da hakan daga jami’an tsaro, sai dai kuma rahotanni na cewa matasan sun rufe unguwar ba shiga ba fita.

 

 


Post a Comment

Previous Post Next Post