Sanatocin arewacin Nijeriya sun bukaci ECOWAS ta janye takunkumin da ta kakaba wa Jamhuriyar Nijar

Sanatoci daga arewacin Nijeriya sun bukaci kungiyar ECOWAS da ta janye takunkumin da ta kakaba wa Jamhuriyar Nijar bayan da sojoji suka hambarar da gwamnatin farar hula a watannin da suka gabata.

A watan Juli da ya gabata na shekarar 2023 ne dai sojoji suka gudanar da juyin mulkin da ya hambarar da gwamnatin Bazoum Mohamed a Jamhuriyar Nijar.

Daga cikin takunkuman da aka sanya wa Nijar din akwai na yanke duk wata alakar kasuwanci tsakaninta da kasashen da ke cikin kungiyar ta ECOWAS, sai Nijeriya ta yanke wutar lantarkin da take ba Nijar sai kuma kasar Ivory Coast ta yanke duk wata alakar shige da ficen kaya tsakaninta da Nijar.

Sanatocin bayan wata ganawa da suka yi a Abuja, sun bukaci da ECOWAS ta janye wannan takunkumin da ta kakaba wa Jamhuriyar Nijar.

Sannan sanatocin sun bukaci sojojin Nijar da su saki tsohon shugaban kasar Bazoum.

Post a Comment

Previous Post Next Post