Gwamna Dikko ya ware Naira bilyan 17 don biyan fansho da giratuti a shekarar 2024

Gwamnan jihar Katsina ya gabatar da daftarin kasafin kudin shekarar badi, 2024 na Naira bilyan 454,308 a gaban Majalisar dokokin jihar.

Bangaren ilmi dai ne ke da kaso mai tsoka a cikin kasafin kudin da Gwamnan ya gabatar da ke da kaso 20.13%.

Da yake yi wa manema labarai Karin haske game da abin da ke kunshe cikin kiyasin kasafin kudin, kwamishinan kasafin kudi na jihar Katsina Bello Hussaini Kagara, ya ce idan an kwatanta da kasafin kudin shekarar ta 2023, na shekarar badi, 2024 ya karu da Naira bilyan 153.

Ya yi karin hasken cewa za a biya albashin Naira bilyan 38, a shekarar 2024 sai giratuti da fansho gwamnatin ta kiyasta za ta kashe Naira bilyan 17b.

Kwamishina Bello Hussaini Kagara ya ce manyan ayyuka na da kaso 72% sai kaso 27% na ayyukan yau da kullum.

Wannan ne dai karon farko da Gwamnan ya gabatar da daftarin kasafin kudi a matsayin Gwamnan jihar Katsina bayan da ya yi nasara a babban zaben 2023.

Tsohon Gwamna Masari a cikin watan Nuwambar 2022, ya gabatar da kasafin kudin Naira bilyan 288 a gaban Majalisar dokokin jihar Katsina, da ya zamo shi ne na karshe a kwanakin mulkinsa da ya shafe shekaru 8 yana gudanarwa a jihar Katsina.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp