Muna bakin cikin halin da jihar Zamfara ke ciki - Masu rajin 'yancin Dan'adam

Shugaban kungiyar mai rajin kare hakkin bil'adama Comrade Abraham Ekokotu ya bayyana cewa sun shirya wannan taron ne a yau litinin 27 ga watan nuwamba 2023, domin yin karin haske kan halin da jihar Zamfara ke ciki da kuma yin kira da a dauki matakin gaggawa.. 

Ya kara da cewar wannan kungiyar tasu ta Gamayyar kungiyoyin farar hula da masu kare hakkin jama'a a Najeriya (CoCSPION) na kan wani aiki na kasa baki daya domin zakulo hazikan gwamnoni a Nigeria da kuma Gwamnonin da suka gaza cimma abinda sukayi alkawari a lokacin yaqin neman zabe, ya kara da cewar a yau kungiyarsu ta isa jihar Zamfara, inda suka gamu da wani mawuyacin halin da jihar take ciki karkashin mulkin gwamna dauda lawal dare.. 

Sakataren kungiyar ya bayyana cewa, A karkashin jagorancin Gwamna Dauda Lawal Dare, Jihar Zamfara na fama da matsaloli da dama da suka hadar da rashin tsaro, rashin aikin yi, fatara, tabarbarewar tattalin arziki da rashin isassun kayayyakin more rayuwa da kuma matsalar karancin ababen more rayuwa. Hakki ne akanmu a matsayinmu na yan kasa mu jawo hankali ga waɗannan batutuwa masu mahimmanci da kuma ba da shawara domin kawo canji mai kyau.

Tsawon watanni 8 da suka gabata al’ummar jihar Zamfara na cikin mayuyacin hali sakamakon gazawar sabuwar gwamnati wajen cika alkawarin data dauka lokacin yakin neman zabe, yayi alkawarin kawo karshen matsalar tsaro a kasa da hour 24 idan tayi tsamari sati daya, amma adadin mutanen da aka kashe ko aka sace ya linka adadin mutanen da aka kashe a zamfara a gwamnatocin baya sau uku, Wannan mummunan tashin hankali ya jefa al’ummar Zamfara cikin fargaba.. 

Bugu da kari, rashin mayar da hankali kan manyan ayyuka, sannan kuma yazo ya fara korar jami’an gwamnati wanda hakan ya kara dagula lamarin. Al’ummar Zamfara na fama da matsanancin talauci, wanda hakan ya tilasta musu yin hijira daga gidajensu domin neman ingantacciyar rayuwa. Wannan gudun hijirar dai wata alama ce da ke nuna gazawar gwamna wajen biyan bukatun al’ummar da suka zabeshi.

Duk da tsananin talauci da jama’a ke fuskanta, gwamnan ya kashe sama da Naira miliyan 400 wajen tafiye-tafiyen kasashen waje a cikin watanni uku kacal.

Wannan makudan kudaden da ake kashewa a tafiye-tafiyen kasashen ketare na haifar da ayar tambaya game da inda gwamnatin zamfara ta sa gaba, A yayin da al’ummar Zamfara ke fafutukar ganin sun samu tsaro da kuma abinda zasu ci, abin takaici ne ganin yadda gwamnatin ta kashe makudan kudaden al’umma wajen yin abubuwan more rayuwa maimakon magance matsalolin da jihar ke fuskanta.

CoCSPION ta yi kakkausar suka kan wannan almubazzaranci da dukiyar al’umma tare da yin kira ga kungiyoyi da duk wata ma’aikata ta gwamnati datake da iko, da yan majalissu domin kawo karshen wannan almubazzaranci da kudin alumma bata hanyar daya dace ba. Al'ummar Zamfara sun cancanci shugaban dazai fifita jin dadin su da kuma hanyoyin da za su inganta rayuwarsu, maimakon kashe kudaden tafiye-tafiye fiye da basuda wani amfani ga talakawan jihar zamfara.. 

Muna kira ga hukumomin da abin ya shafa da su binciki lamarin sosai tare da daukar matakin da ya dace don ganin an yi amfani da dukiyar al’umma domin ci gaban al’ummar Jihar Zamfara.

A yau mun tsaya tsayin daka wajen ganin mun janyo hankalin yan kasa domin susan halin da al'ummar jihar Zamfara suke ciki, gazawar wannan gwamnatin ta Dauda lawal Dare a bayyane take, kuma ya zama wajibi a garemu a matsayinmu na yan kishin kasa, mu fito mu bayyanawa duniya halin da gwamnatin jihar zamfara ta sakasu a ciki! 

Daga karshe Muna kira ga al’ummar duniya, hukumomin gwamnati, da ‘yan kasa da abin ya shafa da su hada kai da mu wajen neman a dauki matakin gaggawa da kawo sauyi ga al’ummar jihar Zamfara. Mu hada kai mu ɗaga murya kuma mu tabbatar da cewa an samu sauyi na gaggawa a jihar zamfara ba tare da bata lokaci ba….

Post a Comment

Previous Post Next Post