Wasu gungun mutane da ale kyautata zaton 'yan ta'adda sun kai hari a kauyen gada na karamar hukumar Bungudu ta jihar Zamfara, suka kashe mutane 7.
Kazalika, rahotanni sun ce, 'yan bindigar sun kuma raunata wasu mutane da dama a yayin harin da suka kai da yammacin Asabar.
Wani mazaunin garin da Radio Nigeria ta zanta da shi, ya ce mutanen sun je kauyen a bisa babura dauke da muggan makamai, suna harbin kan mai uwa da wabi har ma suka yi garkuwa da wasu.
Wannan harin dai na zuwa ne kwana daya, bayan da Gwamna Dauda ya bar jihar zuaa jihar Imo don hidimar zaben Gwamna da ke gudana a halin yanzu.
Kawo lokacin hada wannan labari dai babu wata sanarwa a hukumance daga jami'an tsaro.