Mun himmatu don yaki da cin zarafin mata - Gwamnatin Sokoto

Yayin da aka kammala aikin shirin kawo karshen cin zarafin mata na Kungiyar Tarayya Turai (EU) da Majalisar Dinkin Duniya tare da mikawa ga masu ruwa da tsaki, Gwamnan Jihar Sokoto, Dr Ahmed Aliyu, ya bayyana cewa bisa tallafin shirin, gwamnatin jihar ta inganta kula da wadanda suka tsira daga Cin Zarafi na Jinsi (SGBV) a cikin jihar.

"Mun inganta ayyukan kula da waɗanda suka tsira daga cin zarafi na Jima'i saboda bambancin jinsi (SGBV) kuma mun tabbatar da cewa mata da 'yan mata sun sami damar samun kulawar da suke buƙata don sake gina rayuwarsu." Ya bayyana hakan ne a wajen taron kammala shirin tare da mika cibiyar da aka samar ga Gwamnatin Jihar Sokoto, a ranar 11 ga watan Nuwamba, 2023, a dakin taro na kasa da kasa da ke Sokoto.

Gwamnan wanda ya samu wakilcin shugaban ma’aikatansa, Alhaji Aliyu Dikko, ya jaddada cewa “jihar ta yi namijin kokari wajen tabbatar da cewa mata da ‘yan mata sun samu kulawar da ta dace, tare da saukaka yunkurin farfadowa don sake gina rayuwarsu bayan da suka tsallaka siradi.

Ya nanata kudurin jihar na kawar da cin zarafi da munanan ayyuka da ake yi wa mata da ‘yan mata, ya kuma jaddada gagarumin ci gaban da aka samu ta hanyar shirin mai lakabin ‘Spotlight Initiative’, wanda ya kasance wani cikakken shiri da aka tsara don tabbatar da cewa kowace mace walau babba ko yarinya za ta iya rayuwa a Jihar Sokoto ba tare da fuskantar wani tashin hankali da abubuwa na cin zarafi ba.

“Gwamnati ta himmatu wajen samar da dokoki da tsare-tsare da za su kare mata da ‘yan mata, tare da samar da yanayin da zai tabbatar da yin hukunci da adalci ga wadanda suka tsira daga cin zarafin mata a Jihar Sakkwato.” Ya bayyana.

Babban jami’in kula da kananan yara na Asusun UNICEF, Ibrahim Sesay, wanda ya wakilci Majalisar Dinkin Duniya a wajen taron ya ce, “A cikin shekaru biyar da suka gabata, tare da hadin gwiwar gwamnatin Jihar Sokoto, shirin na ‘Spotlight Initiative’ ya samu gagarumar nasara wajen magance matsalolin da suka shafi cin zarafin mata (GBV) da sauran munanan dabi’u da miyagu ke aikatawa a kan mata manya da yara."

Ya bayyana wasu muhimman nasarorin da shirin ya samu kuma da suka hada da: samar da dokar kariya ga yara, da kafa Cibiyar Kula da Wadanda Suka Tsira Daga Cin Zarafi (GBV), da yaye sama da mata 9,000 da aka koyar a karkashin shirin ilimi na musamman da aka tsara ga wadanda ba su yi karatu ba.

Sesay ya jaddada yawaitar abubuwan da ba su dace na zamantakewar al’umma da ake yi kamar aurar da ‘ya’ya mata da wuri, da kaciyar mata a Jihar Sakkwato, yayin da a cewarsa, har yanzu Nijeriya na ci gaba da fama da wadannan matsaloli da suka hada da aurar da ‘ya’ya mata kanana su miliyan 26 da wasu miliyan 19.9 da suka sha da kyar sanadin yi musu yankan gishiri.

“Wannan biki na rufewa ya zama kira ga masu ruwa da tsaki da su jajirce wajen ganin sun kare hakkin mata da yara a Jihar Sakkwato. Har ila yau, shirin yana bukatar gwamnati ta ware wani kaso na kudi tare da ba da fifiko ga kare yara da inganta daidaito tsakanin jinsi da karfafa mata.”

Kwamishiniyar kula da harkokin mata da yara na Jihar Sokoto, Hajiya Hadiza Ahmed Shagari ta bayyana cewa kare lafiyar mata da ‘yan mata na da matukar muhimmanci a Jihar Sokoto, don haka ne aka kafa wata cibiya mai suna ‘Nana Kadija Centre’.

Kwamishiniyar wadda babbar sakatariyar ma’aikatar, Hajiya Aisha Mohammed ta wakilta, ta bayyana cewa, “Mun samu nasara tare da yin aiki tare da dukkan abokan hulda na hukumomi, da kungiyoyi masu zaman kansu wadanda suka jajirce wajen gudanar da ayyuka daban-daban na magance cin zarafin mata da kuma kare yara a Jihar Sokoto."

Alkalin Alkalan Jihar Sokoto, Hon. Mai shari’a Muhammad Sifawa, wacce Hajiya Mariya Haruna ta wakilta, ya bayyana jin dadinsa ga hukumar shari’a ta Jihar da kungiyar Tarayyar Turai da Majalisar Dinkin Duniya bisa goyon bayan da suka bayar tun bayan fara aikin a shekarar 2019.

Ya ce, “Ma’aikatar shari’a ta kuduri aniyar dagewa a kokarinta na ganin an gaggauta gudanar da shari’a kan laifukan da suka shafi cin zarafi na jinsi (GBV) da kuma munanan halaye, don tabbatar wa mata da 'yan mata cewa akwai wani wuri mai aminci da za su iya kai kokensu duk lokacin da suke buƙatar hakan."

Shirin na haɗin gwiwar ‘EU da UN Spotlight Initiative’, na da nufin kawar da cin zarafin mata da 'yan mata da yaki da abubuwa masu cutarwa a Nijeriya, inda ya yi tasiri mai mahimmanci tun lokacin da aka kafa shi a 2019. An aiwatar da shirin cikin nasara a jihohi biyar: Adamawa, Kuros-Riba, Ebonyi, Legas, Sokoto, da kuma Babban Birnin Tarayya Abuja.

Post a Comment

Previous Post Next Post