Tsohon shugaban kasa Buhari ya yaba da aikin kwastam a Katsina


Tsohon shugaban Nijeriya Muhammad Buhari ya yaba da babban jami'in hukumar kwastam da ke kula da jihar Katsina Mohammed Umar da ya ke tsoma al'ummar gari a yaki da 'sumoga' a sassan jihar.

Tsohon shugaban kasar ya na magana ne a lokacin da ya karbi bakuncin babban jami'in na kwastam a gidansa da ke Daura jihar Katsina.

Ya kuma yaba da yadda ake samun hadin kai tsakanin hukumomi domin yaki da ta'addanci.

Tsohon shugaban kasar ya ce batun tsaro abu be da ya shafi kowa da kowa, ya shawarci al'umma da su rika ba jami'an tsaro bayanai sahihai domin kasa ta zauna lafiya.


Post a Comment

Previous Post Next Post