Tsaron rayuka da dukiyoyin al'ummar jihar Zamfara ne a gabana - Gwamna Dauda

Gwamnan jihar Zamfara Dauda Lawan Dare ya ce har yanzu bai yi kasa a guiwa ba wajen tabbatar da rantsuwar da ya sha ta kare rayuka da dukiyoyin al'ummar jihar Zamfara.

Dauda Lawan Dare na magana ne a Masarautar Maru ta jihar da ya je ziyarar ta'aziyya da jajantawa bisa hare-haren ta'addanci da suke fama da su.

Gwamnan ya yi ta'aziyya ga Masarautar da daukacin al'ummar wannan masarauta bisa ayyukan ta'addanci da ke wakana ga al'ummar yankin.

A yayin ziyarar, Gwamnan tare da Mai Martaba Sarkin Maru Alhaji Abubakar Gado sun gudanar da sallar Juma'a a babban masallacin garin, inda aka gabatar da addu'o'i na samun zaman lafiya a yankin da ma jihar bakidaya.

Post a Comment

Previous Post Next Post