'Yan bindiga na tursasa wa wasu manoma a wasu kauyukan jihar Kaduna su biya haraji kafin su kyale su, su girbe amfanin gonakinsu da suka noma a daminar bana.
Kauyukan da lamarin ya shafa sun hada da na Kidandan da Galadima a karamar hukumar Giwa, sai mutanen kauyen Angular Fala'u da na Kerawa suka ce kodayaushe 'yan ta'addar na yin garkuwa da su a duk lokacin da suka je girbin amfanin gonakinsu.
Wani mazaunin kauyen Kidandan Malam Jamil, ya ce al'ummar kauyensu na biyan kudin harajin da suka kai Naira 70,000 zuwa 100,000 don su girbe amfanin gonakinsu.
Ya ce wadanda suka ki ko gaza biya, za a sace su ko a kashe ko kuma 'yan bindigar su kwace amfanin gonakin.