Hukumar CCB za ta gurfanar da Muhyi Magaji Rimin Gado

Hukumar kula da da'ar ma'aikata ta Code of Conduct Bureau, ta sanar cewa ta kammala dukkanin shirye-shirye na gurfanar da shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano da aka fi sani da 'Anti Corruption' a gabanta.

Hukumar kamar yadda jaridar Daily Trust ta rawaito, ta sanar cewa a ranar Alhamis ta makon gobe 16 ga Nuwamba ne hukumar za ta gurfanar da Barr Muhyi.

Wata majiya daga hukumar ta ce za a gurfanar da Barr Muhyi ne bisa zargin wasu laifuka na gaza mika mata rubutaccen bayani game da kadarorin da ya mallaka da sauran laifuka.

A wani sammace da Magatakardan hukumar ya aike wa shugaban hukumar, an umurce shi da ya bayyana a gabanta domin amsa wasu tuhume-tuhume guda 10.

Post a Comment

Previous Post Next Post