Kimiyya ta taimaka wajen rage yaduwar Corona da sauran cutuka - UNESCO


Darakta Janar ta Hukumar Bunkasa Ilimi da Al’adu ta Duniya (UNESCO), Ms. Audrey Azoulay, ta jaddada tasirin da kimiyya ke da shi wajen samar da ingantacciyar duniya. 

Ta bayyana haka ne a cikin wani sakon da ta gabatar na bikin ranar kimiyya ta duniya don haɓaka zaman lafiya da ci gaba a ranar 10 ga Nuwamba, 2023.

A cewarta, kimiyya ta taimaka wajen rage yaɗuwar cututtuka kamar COVID-19, baƙon dauro, da foliyo ta hanyar samar da allurar rigakafi.

Haka kuma, ta ce UNESCO na tunawa da ranar Kimiyya ta Duniya ce don inganta zaman lafiya da ci gaba a kowace shekara tare da jaddada muhimmancin da kimiyya take da shi. 

A bana, bikin ya ninka sau biyu, yayin da ya zo daidai da lokacin bikin shekarar ilimi ta ƙasa da ƙasa don samar da ci gaba mai ɗorewa, wadda daga bisani za ta shiga cikin shekaru goma na kimiyyar ƙasa da ƙasa don ci gaba mai dorewa daga 2024 zuwa 2033.

Bugu da ƙari ari, Ms. Azoulay ta bayyana jajircewar UNESCO wajen tallafa wa bincike na kimiyya, wanda aka misalta ta hanyar shawarwarinta na 2021 a kan haɓaka kiniyy.

“UNESCO tana aiki domin haɓaka daidaiton jinsi a fagen kimiyya, gami da shirye-shirye a Afirka da Caribbean tare da haɗin gwiwar gidauniyar L'Oréal.

“A cikin shekarun da suka gabata, wannan hadin gwiwa ya karfafa ayyukan masana kimiyya, mata fiye da 4,100 da suka fito daga kasashe sama da 110”. In ji ta.

Wannan shi nebabban jigon ranar Kimiyya ta Duniya ta wannan shekara kuma za ta kasance jigon taron ministocin da zai gudana a hedikwatar UNESCO a ranar 13 ga Nuwamba, 2023. 

Manufar wannan taron shi ne a karfafa dogaro ga kimiyya ta hanyar magance mishkiloli da suka jiɓanci ilimin kimiyya, sada kimiyya daidai da bukatun al'umma, da kuma ba da kariya da tabbatar da 'yancin masana kimiyya.

Post a Comment

Previous Post Next Post