Hisbah a Kano ta kori wani jami'inta

Hukumar Hisbah a jihar Kano ta sanar da korar daya daga cikin ma'aikatanta bayan samunsa da laifin yi mata zagon-kasa a yakin da take yi da aikata badala a jihar.

Babban kwamandan hukumar Shekh Aminu Daurawa ya sanar da hakan ga manema labarai a Kano, inda ya ce akwai karin wasu jami'ai biyar da ake bincike a kansu.

Ya ce mutumin da aka kora din na hada baki da bata-gari wajen kitsa wata kitimirmira a jihar.

Sheikh Daurawa ya ce tun bayan nada shi kwamandan Hisbah, ya dukuba wajen tsaftace ayyukanta ta hanyar zakulo bare-gurbi.

Post a Comment

Previous Post Next Post