'Yan sanda sun kama matashin da suka ce ya shahara wajen satar awaki a Kaduna

Rundunar 'yan sandan jihar Kaduna ta sanar da kama wani da ake zargi ya shahara a satar awaki a kauyen pasali Konu na karamar hukumar Kagarko ta jihar.

Mai magana da yawun rundunar 'yan sandan ASP Mansur Hassan ya shaida wa kamfanin dillancin labaran Nijeriya NAN cewa an kama wanda ake zargin ne a ranar Asabar.

'Yan sandan sun ce 'yan sintirin Vigilante na yankin ne suka kama matashin mai kimanin shekaru 20 da ya fito daga kauyen Igwa na karamar hukumar a lokacin da suke sintiri da dare suka hannanta shi ga 'yan sanda.

Mai magana yawun rundunar 'yan sandan ya ce a lokacin da aka kama matashin, an same shi da muggan makamai, sannan kuma ya saka takunkumin rufe fuska na facemask.

Post a Comment

Previous Post Next Post