Kotu ta sauke Gwamnan Plateau na PDP ta ba na APC


Kotun daukaka kara da ke zamanta a Abuja ta soke zaben gwamna Caleb Muftwang na jihar Filato.

Kotun ta ce zaben na gwamnan wanda dan jam'iyyar PDP ne bai inganta ba kamar yadda ta bayyana a Lahadin nan. 

Kotun ta kuma umurci Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) da ta janye takardar shaidar cin zabe da aka baiwa Muftwang tare da ba Goshwe na APC sabuwar takardar shaidar lashe zabe.

Post a Comment

Previous Post Next Post