'Yan ta'adda na tilasta wa manoma biyan haraji kafin girbe amfanin gona a Kaduna

Wasu mazauna yankuna karkara a jihar Kaduna na kokawa kan yadda 'yan bindiga ke kakaba musu haraji kafin su kyale su, su girbe amfanin gonakinsu.

Manoman musamman na yankunan kananan hukumomin Giwa, Birnin Gwari da Igabi sun ce suna samun tsaiko da razani mai yawa daga 'yan ta'adda a yankin a daidai lokacin da suke kokarin girbe amfanin gonakinsu.

Bayanan da jaridar Daily Trust ta samu, sun ce da yawa daga cikinsu ma sun bar zuwa gonakin saboda barazana kisa ko sacewa daga 'yan ta'adda.

Hakan na zuwa ne duk kuwa da kokarin jami'an tsaro wajen kakkabe ayyukan ta'addanci a yankunan. Amma dai hakan ba ta sa manoman sun samu sukunin kawar da amfanin gonakinsu ba, da wasu lokuttan ake sanya musu tilas su biya haraji kafin a bari su je gonakin.

Yankunan sun hada da kauyen Kidandan, Galadimawa Kerawa, Sabon Layi, Sabon Birni da Ruma, inda bayanai suka ce manoman a yankunan na biyan harajin 70k-100k ga 'yan ta'adda kafin a bari su je gonakin.

Bayanai dai sun ce wadanda suka ki biyan wadannan kudaden kuwa na fuskantar barazanar sacewa, kisa ko kuma cinye amfanin gonakinsu.

Wani mazaunin yankin ya shaida cewa wannan lamari da ya yi kamari ya sa mutane da yawa sun fara shawarar yin hijira zuwa wasu garuruwan.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp