Sojoji da DSS sun bankado wani yunkurin kai hari a Kano

Rundunar sojin Nijeriya hadin guiwa da jami'an tsaron ciki na DSS sun dakile wani yunkurin kai hari a karamar hukumar Gezawa ta jihar Kano.

Jami'an hukumomin biyu dai sun gudanar da aikin dakile harin da aka tsara da sanyin safiyar Juma'a, inda suka kama mutane biyu da ake zargi da kokarin kitsa harin.

A cikin wata sanarwa daga daraktan yada labarai na rundunar sojin Nijeriya Nwachukwu Onyeama, ta ce a yayin samamen, an yi nasarar kwato bindigu samfurin AK 47 guda biyar, da sauran kayan kai hari.


Post a Comment

Previous Post Next Post