Mun gamsu da jagorancin Kwankwaso a tafiyar NNPP - Jiga-jigan KwankwasiyyaShugabannin Jam'iyyar NNPP Na Ƙasa Reshan Arewa Maso Yamma Ƙarƙashin Jagorancin Hon. Shehu M. Bello (Shehun Garu) Sun Gudanar Da Taro A Jihar Kaduna.

Taron shugabancin jam'iyyar ta NNPP reshen arewa maso yamma tare da masu ruwa da tsaki na shiyyar a jiya a Kaduna sun gudanar da taro na musamman inda ya haɗa da mataimakin gwamnan jihar Kano, yan majalisun jiha, tare da manyan kwamishinoni.

Maƙasudin taron shine kaɗa "Kuri'ar Amincewa" da Shugaban Kasa kuma Dan Takarar Shugaban Kasa na Jam'iyyar NNPP a 2023- Sanata Engr Rabi'u Musa Kwankwaso, Kwamitin Ayyuka na kasa kuma Shugaban riko na NNPP na kasa.

 Hakan dai na zuwa ne jim kadan bayan wasu sun sanar da fitar da Jam’iyyarsu ta kasa daga jam’iyyar.

Haka kuma shugabannin shiyyar Arewa maso Yamma sun yi alkawarin ladabtar da duk wanda aka kama yana aikata irin wannan aika-aika a cikin jam’iyyar.

 Mahalartan sun taya Gwamnan Jihar Kano murna bisa duk wani kyakkyawan aiki da yake yi na kokarin cika dukkan wani alkawari da ya dauka.

Haka-zalika sun kuma taya mambobinsu a Majalisar Dokoki ta kasa murnar samun wasu kujerun manyan kujeru masu yawa da suka haɗar da kujerun Chairman da mataimakansu.

Sun kuma taya 'yan majalisar wakilansu murnar samun nasara a kotuna da kuma wadanda suka samu nasara a kotun daukaka kara.

 A karshe sun jaddada cewa duk waɗannan nasarori sun samu ne saboda jajircewa irinta shugabansu kuma jagoransu a matakin kasa baki daya, tare da shugaban mu na kasa a NNPP hakan ke ƙara bamu cikakken numfashi!  Haka idan kuma ba tare da shi ba, to ta mutu baki daya.

Post a Comment

Previous Post Next Post