Rundunar 'yan sandan jihar Katsina ta sanar cewa jami'anta sun yi nasarar dakile kokarin sata da garkuwa da wani mutum mai suna Tukur Adamu na kauyen Masaku cikin karamar hukumar Kankara ta jihar.
Mutumin mai shekara 40, kamar yadda sanarwar da ta fito daga mai magana da yawun rundunar 'yan sandan ASP Aliyu Abubakar Sadiq ta ce hakan ta faru ne bayan samun kiran gaggawa da jami'anta suka yi, cewa masu garkuwa da mutane na yunkuri baje hajarsu a kauyen Masaku, amma cikin lokaci suka je suka dakile wannan yunkuri har suka ceto wannan mutumi ba tare da ya rasa ransa ba.
Sai dai sanarwar ta ce mutumin ya samu rauni ta dalilin harbin bindiga, amma dai an garzaya da shi asibiti, yanzu haka yana karbar magani.
Sanarwar ta ce kwamishinan 'yan sandan jihar CP Aliyu Abubakar Musa ya yaba da irin kwazon jami'an da suka ceto mutumin, ya kara da cewa 'yan sanda a jihar Katsina ba za su yi kasa a guiwa ba wajen tsare rayuka da dukiyoyin al'ummar jihar.