SERAP ta maka Shugaba Tinubu kotu kan wasu kudade

Kungiyar nan da ke rajin ganin an tabbatar da adalci ta SERAP ta kai karar shugaban Nijeriya Bola Tinubu bisa zargin ya gaza bincikar zargin yin wadaka da kudaden gyaran matatun man kasar nan da karin wasu kudade da aka samu daga man fetur a shekarun 2020 da 2021.

Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa mataimakin daraktan kungiyar Kolawole Oluwadare da aka raba wa manema labarai a Abuja.

Wannan zargi na Shugaban kasa ya gaza bincikar wadannan kudade dai na cikin wani rahoto da kungiyar tabbatar da gudanar da adalci a tsakanin masana'antu ta fitar a shekarar 2021.

Oluwadare ya ce kungiyar na neman kotu ta tilasta wa Shugaban kasa, cewa ya umurci hukumomin yaki da cin hanci da rashawa na su binciki kamfanin NNPC kan wannan batu.

A cikin takardar karar da suka shigar mai lamba FHC/L/CS/2334/2023, SERAP na son kotu ta ba Shugaba Tinubu umurni kamar yadda kundin mulkin kasa ya tanadar na a binciki kudin da suka kai Dala bilyan 15 na kudaden shigar da aka samu ta bangaren man fetur da Naira bilyan 200 da aka kasafta don gyaran matatun man kasar nan da suka yi batan-dabo.

Post a Comment

Previous Post Next Post