'Yan bindiga sun bude wuta kan masu Mauludi a Katsina, sun kashe kusan 20 sun sace da dama.

'Yan bindiga da ba a san adadinsu ba, sun afka kauyen Kusa da ke cikin karamar hukumar Musawa a jihar Katsina cikin daren Lahadi, inda suka hallaka mata da kananan yara sama da 20.

'Yan bindigar da suka farmaki inda ake taron Mauludi, sun kuma yi awon-gaba da mutanen da ba a san adadinsu ba a halin yanzu.

Bugu da kari, rahotannin da jaridar Daily Trust ta tattara sun ce karin wasu mutane kusan 17 sun samu raunuka, inda aka garzaya da wasu babban asibitin Musawa wasu kuma aka nufa da su asibitin kashi na Katsina.

Wani shaidar gani da ido daga garin, ya shaida cewa 'yan bindigar sun bude wa masu taron Mauludin da misalin karfe 11:05 na daren Lahadi.

Ya ce kafin jami'an tsaro su kawo dauki, maharan sun tsere , ba a tarar da ko daya ba.

Rundunar 'yan sandan jihar Katsina ta hannun mai magana da yawunta ASP Aliyu Abubakar Sadiq, ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce maharan sun raunata kusan mutane 18.

Post a Comment

Previous Post Next Post