Ministan Tinubu ya yi nasarar zama Sanata a kotun daukaka kara

Kotun daukaka kara da ke zamanta a Abuja ta tabbatar wa da Simon Bako Lalong kujerar Sanatan da ke wakiltar Plateau ta Kudu a majalisar dattawan Nijeriya.

Simon Lalong dai shi ne ministan kwadago a gwamnatin Bola Ahmad Tinubu, da ya yi takarar Sanata a karkashin jam'iyyar APC.

Kotun ta yi watsi da bukatar Napoleon Bali na jam'iyyar PDP.

Dama dai kotun sauraren kararrakin zabe ta ayyana Simon Lalong a matsayin wanda ya yi nasarar bayan da ta yanke hukunci.

Post a Comment

Previous Post Next Post