Mata na cin zarafin maza a 'yan kwanakin nan - NAPTIP

Hukumar da ke yaki da safarar bil'adama ta Nijeriya NAPTIP ta ce ta gano yadda ake samun yawaitar cin zarafin maza ta hanyar tursasa su wajen saduwa a 'yan kwanakin nan.

Shugabar hukumar ta kasa Fatima Waziri Aza ta sanar da hakan a taron bitar da aka shirya a Abuja.

Mrs Fatima ta ce daga cikin matsalolin da mazan ke fuskanta sun hada da raba 'ya'ya da mahaifinsu, korar mazan daga gidan da suke zaune da iyalansu da kuma cusguna musu.

Ta tabbatar wa da mazan da ke cikin wannan kunci da cewa su kwantar da hankulansu, akwai dokar da ta tsare mutuncinsu, inda ta ce sun samu korafe-korafe 15 a cikin wannan shekara da ke nuna yadda aka ci zalin din maza.

Post a Comment

Previous Post Next Post