Tinubu ya gaza wajen yaki da cin zarafin dan adam-Amnesty International


Kungiyar kare hakkin dan adam ta Amnesty International ta zargi shuga Tinubu da kau da idanu game da yadda ake amfani da karfi wajen cin zarafin jama’a a Najeriya.

 

A wata makala da kungiyar ta fitar mai taken tsarin yaki da cin zarafi a Najeriya, ta ce cikin watanni shidan da Tinubu ya yi a Office bai tsinana komai ba, game da yaki da cin zarafin jama’a.

Makalar da kungiyar ta gabatar a Abuja, ta kunshi misalai game da yadda aka ci zarafin jama’a amma gwamnati ta yi shiru.

Amnesty International ta kuma ce abin takaici ne yadda kundin sabbin tsare-tsare da gwamnati ta bijiro da su basu kunshi irin yadda za’a yaki cin zarafin jama’a ba.

Sai dai kuma kungiyar ta ce har yanzu lokaci bai kurewa Tinubu ba, don kuwa yana da damar da zai kawo karshen wannan matsala.

Shawara ta farko da hukumar ta baiwa Shugaba Tinubu shine ya yi kokari wajen tabbatar da ganin an hukunta masu aikata wannan laifi.

 

 

Post a Comment

Previous Post Next Post