Kwace mulki daga hannun Abba gida-gida ka iya tayar da rikicin da zai mamaye Africa- NNPP


 Shugabancin jam’iyyar NNPP ya yi gargadin cewa amfani da karfin iko wajen kwace nasarar da Abba Kabir Yusuf ya samu a jihar Kano, ka iya tayar da hankali, wanda zai iya mamaye Najeriya har ma ya tsallaka zuwa wasu kasashen Africa.

 

Ta cikin wata sanarwa da mai rikon kwaryar shugabancin jam’iyyar Abba Kawu Ali ya sanyawa hannu aka kuma rabawa Kungiyar kasashen yammacin Africa, da ofishin jakadancin Kungiyar tarayyar turai da na kasar Amurka da Burtaniya, ta ce akwai manyan alamu da ke nuna cewa jam’iyyar APC ta lashi takobin yin duk mai yiwuwa wajen kawace mulkin duk da bata yi nasara ba.

Sanarwar ta ce idan aka lura da yadda jihar Kano ke ciki, ana zaman dar-dar ne, saboda yadda jama’ar da suka fita kwan su da kwarkwata suka zabi Abba, amma ake shirin kwace wa, wanda matukar hakan ta tabbata shakka babu zasu iya tayar da rikici.

Sanarwar ta kuma kara da cewa akwai hasashen cewa jama’ar Kano ba zasu yi hakuri irin wanda suka yi a 2019 ba lokacin da aka yi amfani da wasu dokoki wajen kwace mulki kiri-kiri.

Abba Kawu Ali, ya kuma ce akwai bukatar wadannan hukumomi da kasashen duniya su sanya idanu kan wannan shari’a su kuma tabbatar an yi gaskiya, matukar ba haka ba kuma akwai yiwuwar jama’a su dauki doka a hannun su.

Post a Comment

Previous Post Next Post