Jami'ar gwamnatin tarayya ta FUDMA da ke Dutsinma jihar Katsina, ta sanar da cewa daga yanzu duk mai son a dauke shi aikin malanta, sai ya yi digiri na biyu sannan.
Shugaban jami'ar Prof Armaya'u Hamisu Bichi ya sanar da hakan a taron manema labarai, a shirye-shiryen bikin yaye dalibai da jami'ar za ta gudanar.
Ya yi nuni da cewa digirin farko, bai isa a ba mutum aikin malanta a jami'ar ba a halin yanzu, inda ya kara da cewa can baya jami'ar tana ba daliban da suka kammala digirin farko da sakamako mai kyau na first class, saboda a baya jami'ar na kokarin tasowa ne.
Prof Bichi yace jami'ar za ta yaye daliban digirin farko 4,365 da wadanda suka kammala manyan digirori na Post Graduate.
Sannan ya sanar cewa jami'ar za ta karrama manyan mutane uku da digirin girmamawa na 'Honorary Doctorates' da suka haɗa da Sarkin Daura Umar Faruq Umar, Sarkin Bichi Nasiru Ado Bayero da tsohon Jihar Katsina Barr Ibrahim Shema.