Ku janye yajin aikin, mun kama wadanda suka bugi shugabanku, rokon NSA ga 'yan kwadagon Nijeriya


Mai ba shugaban Nijeriya shawara kan harkokin tsaro Malam Nuhu Ribadu ya nemi afuwar 'ya'yan kungiyar kwadago bisa abin da ya kira harin da aka kai wa shugabansu na kasa Comr Joe Ajaero a birnin Owerri na jihar Imo a ranar 1 ga watan Nuwamba, 2023.

Joe Ajaero dai ya isa birnin Owerri ne a ranar domin jagorantar wata gagarumar zanga-zanga, amma aka samu wasu suka lakada masa duka, suka kuma tsare shi na tsawon awanni.

Ba da jimawa ba da faruwar lamarin, kungiyar kwadago ta kasa ta ba gwamnatin tarayya wa'adi da sharudda, ciki hada sai an kamo wadanda suka aikata hakan ga shugaba Ajaero, inda suka yi barazanar tsunduma yajin aiki idan har ba a cika musu wadannan sharudda ba.

Sai dai gwamnatin tarayya ta garzaya kotu, inda ta nemi da a dakatar da NLC daga tafiya wannan yajin aiki, amma dai sai da kungiyar ta tafi yajin aikin a ranar Litinin wayewar Talata. Wannan mataki dai na NLC ya gurgunta harkokin aikin gwamnati a sassa daban-daban.

Sai dai a cikin wata sanarwa daga shugaban sashen yada labarai na ofishin mai shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro Zakari Mijinyawa, ta roki 'yan kwadagon da su yi hakuri su janye yajin aikin don kuwa an kama wadanda suka yi wa shugabansu wannan cin kashi har ma na kaddamar da bincike a kansu.

Malam Nuhu Ribadu ya ce gwamnatin tarayya ta yi nadamar tare da nuna rashin jin dadinta kan wannan lamari da ya faru. Inda ya yi nuni da cewa an taka hakkin bil'adama da hakan ya saba dokar kasa.

Post a Comment

Previous Post Next Post