Kada ku yada karya ko sharri don kare gwamnati, kiran gwamnatin Katsina ga matasan da aka nada mukaman yada labarai


Gwamnatin jihar Katsina ta kare matakinta na nada matasa masu amfani da kafafen sadarwar zamani mukamai daban-daban a gwamnatin, inda ta ce ta yi haka ne don ba al'ummar jihar Katsina damar samun sahihan bayanai daga gwamnati.

Maiwada DanMalam, Darakta Janar na bangaren yada labaran Gwamna Dikko ne ya sanar da hakan a lokacin da aka gayyaci daukacin matasan da aka ba mukaman a gidan gwamnatin jihar domin sanar da su hakkokin da suka rataya kansu.

Maiwada DanMalam ya ce a zamanin dimokradiyya, ana bukatar sanar da al'umma matakai da kudurce-kudurcen gwamnati da hanyoyin da take bi don ta kawo ci gaba da al'umma. Don haka ne, ya ce aka nada wadannan matasa domin su taimaka wajen isar da sakon da gwamnati ke kokarin isarwa ga jama'a da sakon jama'a ga gwamnati.

Ya ce masu ganin kamar an dauki wadannan matasa ne domin su yi yada 'farfaganda' a gwamnatance, Maiwada ya ce sun yi wa abin gurguwar fahimta, domin gwamnatin Malam Dikko, ba wannan layin ta dauko ba.

Darakta Janar din ya ja hankalin matasan da cewa gwamnatin jiha ta aminta da cancanta da jajircewar su ne ya sa aka ba su wadannan mukamai, don haka ya bukace su da su bayyana gaskiya a duk inda suka samu kansu.

Maiwada DanMalam ya tabbatar da cewa za a shirya taron horar da su domin su san makamar aiki da yadda ya kamata su rika aiki cikin kwarewa da gogewa.

DCL Hausa dai ta ba da labarin yadda a kasa da mako daya, Gwamnan Katsina Dikko Radda ya nada matasa sama da 50 mukamai daban-daban a fannin sadarwar zamani.

Post a Comment

Previous Post Next Post