Majalisar dokokin jihar Jigawa ta dakatar da shugabannin kananan hukumomi uku

Majalisar dokokin jihar Jigawa a ranar Larabar da ta gabata ta dakatar da wasu shugabannin kananan hukumomi uku bisa zargin yin balaguro zuwa kasashen waje ba tare da neman izini daga bangaren zartarwa ba. 

Shugabannin kananan hukumomin da aka dakatar sun hada da Mubarak Ahmed na karamar hukumar Yankwashi, sai Rufai Sunusi na Gumel da kuma Umar Baffa na Birniwa wadanda aka ce sun tafi kasar Rwanda.

Rahotannin sun ce kafin tafiyar ta su majalisar jihar ta bayar da umurnin cewa kada shugabannin kananan hukumomin jihar su je ko’ina saboda shirye-shiryen gabatar da daftarin kasafin kudin shekarar 2024 da gwamnan jihar Umar Namadi ke shirin gabatarwa majalisa.


Majalisar ta kuma amince da matakin dakatar da shugabannin kananan hukumomin uku tare da umurtar mataimakansu da su ci gaba da jan ragamar mulkin kananan hukumomin.

Post a Comment

Previous Post Next Post