Ana yaki da Badaru da Matawalle ne domin ture ginshikin nasarar Tinubu a 2027 - Eskimini Bassy


Hadakar kungiyar 'yan kishin kasa daga sassan Nijeriya daban-daban ta ce a tsakanin jihohin arewa maso yamma, Shugaba Tinubu bai da masoya kamar ministan tsaro Mohammed Badaru da karamin ministan tsaro Bello Matawalle, saboda sune mutanen da suka jajirce domin kawo Tinubu akan kujerar shugaban kasa.

Babban jami'in kungiyar Mr Bassy Eskimini na magana ne a lokacin da yake amsa tambayoyi daga 'yan jarida, inda ya yi zargin cewa akwai wasu mutane daga cikin 'yan siyasar Nijeriya da suke yaki da Badaru da Matawalle domin a cire su saboda sun san sune ginshikan Shugaba Tinubu a zaben 2027 mai zuwa.

Mr Bassy ya ce duk duniya ta san cewa cikin wata biyar kacal ministocin tsaro Badaru da Matawalle, sun yi aikin da tun daga shekarar 1999 da aka dawo dimokradiyya, babu wani minista da aka yi a ma'aikatar tsaro wanda ya kawo tsaro cikin gaggawa irin su ba.

Mr Bassy ya buga misali da aikin da sojoji suka gudanar a jihohin Katsina, Sokoto, Kebbi, Zamfara, Neja da Kaduna, inda a nan ne matsalar tsaro take.

 "Amma yanzu ka duba ka ga irin yadda aka samu tsaro yanzu musamman hanyar Zuba zuwa Kaduna, Kaduna zuwa Zaria, Zaria zuwa Funtua, Funtua zuwa Zamfara, Zamfara zuwa Sokoto". 

"Sannan ka duba ka ga irin yadda aka samu tsaro a Zamfara da Sokoto karkashin jagorancin mulkin Badaru da Matawalle a matsayin ministocin tsaro, misali military sun yi ma bandits Ambush rana daya cikin Maru Local Government sun kashe bandit sama 3,000. Kuma an zuba sojoji cikin daji da kan hanya duka fadin Nijeriya kuma suna aiki tukuru. An samu solution babba. Don haka, muna godiya ga wadannan ministoci.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp