Da yiwuwar kudin sayen 'fom' din takarar shugaban kasa na jam'iyyar APC ya kai milyan 250 a zabe na gaba


Akwai alamu da ke nuni da cewa jam'iyyar APC na iya kara kudi a farashin 'fom' din takarar 'yan siyasa a kakar zabe mai zuwa kamar yadda jaridar Daily Trust ta tattaro.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da dama tun farkon kafa jam'iyyar ta APC a 2014, farashin sayar da 'fom' din takara ke ta hauhawa. 

A shekarar 2014 ana tsaka da kakar zaben 2015, jam'iyyar ta sayar da 'fom' din takarar shugaban kasa kan kudi Naira milyan 27.5, sai na Gwamna kan kudi Naira milyan 5.

A zaben 2019 kuwa, jam'iyyar ta APC ta sayar da 'fom' din takarar shugaban kasa kan kudi Naira milyan 45 da Gwamna kuwa Naira milyan 22.5. Bayan nan, a zaben 2023 sai ga 'fom' din ya kai Naira milyan 100 ga mai takarar shugaban kasa da Naira milyan 50 ga masu takarar Gwamna a jam'iyyar.

Wasu jiga-jigan jam'iyyar APC sun yi zargin cewa ana nan ana kokarin kara wa 'fom' din farashi kafin zaben 2027. Sai dai sun yi zargin cewa duk da makudan kudaden da aka tattara, musamman a zaben 2023, har yanzu jam'iyyar ta gaza yin bayanin inda kudin nan suka nufa.

Tsohon mataimakin shugaban jam'iyyar APC mai kula da shiyyar arewa maso yammacin Nijeriya, Salihu Lukman a cikin wata sanarwa, ya koka kan yadda farashin kudin sayar da 'fom' din ke ta kara hauhawa, inda ya yi fargabar APC na iya cazar masu takarar shugaban kasa kudin 'fom' da suka kai Naira milyan 250 da Naira milyan 125 ga masu neman tsayawa takarar Gwamna.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp