'Yan sanda sun kama mijin da ake zargin ya kashe matarsa a Borno

Rundunar ‘yan sandan jihar Borno ta ce a ranar Juma’a jami'anta sun kama wasu mutane biyu, Adamu Ibrahim da Bukar Wadiya bisa zargin kashe wata mata mai suna Fatima Alhaji-Bukar ‘yar shekara 24.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, ASP Sani Kamilu ya bayyana wa manema labarai a Maiduguri ranar Juma’a.

Marigayiyar tana zaune a Dikechiri unguwar Bayan Gidan Dambe a cikin birnin Maiduguri na jihar Borno.

A cewarsa, marigayiyar wadda ke auren Ibrahim, wanda shi ne babban wanda ake zargi da aikata laifin.

Kakakin 'yan sandan ya ce “A ranar 18 ga Oktoba, 2023, wani Adamu Alhaji Ibrahim mai unguwar Dikechiri bayan Gidan Dambe Maiduguri ya ziyarci ofishinsu da ke Gwange tare da rakiyar wani Bukar Wadiya, inda ya kai gawar wata mata wadda ya ce matarsa ​​ce, ya kuma nemi agajin gaggawa daga hukumar. ‘yan sanda,” in ji shi.

Post a Comment

Previous Post Next Post