Jam’iyyar APC ta dakatar da shugabanta na karamar hukumar Roni ta jihar Jigawa Alhaji Sale Idris. Sanarwar da shugaban jam’iyyar ta APC a jihar Hon Aminu Sani Gumel ya fitar ta ce matakin zai ba da dama doka ta yi aikinta a zargin fyade da ake yi wa Alhaji Sale.
Ana dai zargin dan siyasar da yi wa ‘yar aikinsa mai shekaru 14 fyade tuni kuma a cewar jaridar Daily Trust har ta samu juna biyu ta sanadiyyar fyaden da shugaban jam’iyyar na karamar hukumar ya yi mata.
Category
Labarai
Allah ya kyauta
ReplyDelete