Kotun kolin Nijeriya ta ce a ranar 23/10/2023 za ta saurari bukatar da madugun adawa Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP ya gabatar mata domin duba yadda za ta soke nasarar Shugaba Bola Tinubu. Hukumar zabe ta INEC dai ta ayyana Shugaba Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa na 2023. Kotun sauraran kararrakin zabe ma ta tabbatar da wannan nasara ta Tinubu.
Category
Labarai