Tinubu ya soke nadin da ya yi wa matashi Imam Kashim a hukumar FERMA

https://drive.google.com/uc?export=view&id=1zyW1JjmHvrR6uzwlnOTRY4uhTdtM-lwD
Shugaba Tinubu ya soke nadin da ya yi wa matashi dan shekaru 24 Engr. Imam Kashim Imam domin ya jagoranci hukumar gudanarwa (Board of Directors) na hukumar FERMA da ke gyaran hanyoyin gwamnatin Tarayya. Sanarwar da mai magana da yawun shugaba Tinubu, Chief Ajuri Ngelale, ya fitar ba ta bayyana dalilin janye wannan mukami da aka sanar ba da jimawa ba, amma dai nadin matashin ya janyo suka daga bangarori dabam dabam saboda karancin shekarunsa.

Post a Comment

Previous Post Next Post