'Yan sanda sun ceto mutane 4 da aka yi garkuwa da su a Katsina


Rundunar 'yan sandan jihar Katsina ta sanar cewa hadin guiwa da rundunar soji sun yi nasarar ceto mutane 4 da aka yi garkuwa da a su a sassa daban-daban na jihar.

A sanarwar da mai magana da yawun rundunar 'yan sandan jihar ASP Abubakar Sadiq Aliyu ya fitar da DCL Hausa ta samu kwafi, ta ce an yi nasarar ceto mutanen ne a lokacin da jami'an ke aikin sintirin 'patrol' ta wajen kauyen Dankolo na karamar hukumar Dandume ta jihar.

Sanarwar ta rawaito kwamishinan 'yan sandan jihar Katsina CP Aliyu Musa ya yaba wa jami'an da irin aikin da suka gudanar na yadda suka nuna kwarewa wajen gudanar da aikin.

Sannan an kai mutanen asibiti don duba lafiyarsu da tuni an mika su ga iyalansu.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp