Matsin rayuwa ya sa ana samun mutanen da ke kwana 3-4 ba su ci abinci ba - Mustapha Inuwa

Tsohon Sakataren Gwamnatin jihar Katsina Mustapha Muhammad Inuwa ya ce yanzu ana wani yanayi na matsin rayuwa da har ta kai mata na cewa mazajensu sun rasu don a taimake su alhali mazan na nan da ransu.

Mustapha a wata zantawa da ya yi wasu kafafen yada labarai na zamani a Katsina, ya ce yanzu haka ana samun mutanen da ke kwana 3-4 ba su ci abinci ba, hasalima, ba su kirguwa a cikin al'umma a wannan yanayin da ake ciki.

Mustapha Inuwa wanda ya yi wa APC takarar Gwamna a jihar Katsina a zaben 2023, ya koka kan irin halin karancin tsaro da sassan jihar ke fama da shi, inda ya yi addu'ar duk masu amfana da yanayin matsalar tsaro da ake ciki, "muna addu'ar Allah Ya yi mana maganinsu".

Ya koka cewa idan aka ci gaba da tafiya haka a kasar nan, ba a san halin da 'ya'ya da jikoki za su shiga ba a rayuwarsu ta gaba.

Mustapha Muhammad Inuwa ya ce "Ni dan siyasa ne, ba dan takara ba. Tun daga lokacin da aka kammala zabe, har ya zuwa yanzu, ban taba tafiyar da na kwana bakwai bani Katsina ba. Kuma ina iya wata biyu cur, ban bar Katsina ba. Gidana a bude yake ga kowa, haka ofis dina, duk rana sai na je".

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp