Ana fatar yi wa jarirai 797,209 rajista a Katsina

Hukumar kidayar al'umma ta Nijeriya hadin guiwa da Asusun kula da kananan yara na majalisar dinkin duniya UNICEF sun kuduri aniyar yi wa jarirai 797,209 rajistar haihuwa a jihar Katsina.

Jami'ar Asusun UNICEF Mrs Ogbodo Adaku ta sanar da hakan a lokacin taron horar da wadanda za su yi aikin rajistar a ranar Asabar.

Ta ce kusan ma'aikatan wucin-gadi 1,083 ne za su yi aikin rajistar a fadin mazabu 361 da ake da su a kananan hukumomi 34 na jihar.

Mrs Adaku ta ce za a yi wannan aikin kidayar jarirai a jihohi 23 hada babban birnin tarayya, Abuja.

Ta kara da cewa ana kokarin ganin an yi wa yara milyan 12 rajista a fadin Nijeriya.

Post a Comment

Previous Post Next Post