Yunkurin tsige Gwamnan jihar Rivers Sim Fubara ya sa an sauke jagoran majalisar dokokin jihar (House Leader) Edison Ehie da sanyin safiyar Litinin din nan.
Dama dai a 10pm na daren Lahadi, wata gobara ta tashi a ginin majalisar da har yanzu ba a san musabbabin tashin ta ba.
Gwamnan jihar ta Rivers Sim Fubara ya ziyarci majalisar da sanyin safiyar Litinin, inda 'yan majalisar kowa ya watse a lokacin da aka fara harba hayaki mai sa hawaye na 'tear gas'.