'Yan bindiga sun sace dalibai mata na Jami'ar FUDMA, Katsina

Wasu mutane dauke da makamai sun mamaye gidajen kwanan daliban jami'ar Gwamnatin tarayya da ke Dutsinma, FUDMA jihar Katsina suka sace dalibai mata guda biyar kamar yadda DCL Hausa ta samu labari.

Lamarin da ya faru da misalin karfe biyu na daren Talata wayewar Laraba, ya faru ne a gidajen kwanan daliban da ke bayan makarantar Mariamoh Ajiri, a inda daliban suka kama hayar gidajen da suke kwana.

Ya zuwa yanzu dai babu takamaiman bayanin asalin jihohin da suka fito da kwasa-kwasan da suke karantawa da azuzuwan da daliban suke. Kazalika, babu cikakken bayanin halin da daliban mata suke ciki a halin yanzu, don babu tabbacin ko 'yan bindigar sun kira waya suna neman kudin fansa ko a'a.

Ko a kwanakin baya, wasu dalibai 'yan jami'ar ta FUDMA sun taba fadawa irin wannan hali, inda wasu 'yan bindiga suka yi awon-gaba da dalibai biyu a gidajen kwanan da suka kama haya bayan ginin gidan rediyo na Dutsinma.

Ko a makonni biyu da suka gabata, wasu 'yan bindiga sun shiga jami'ar gwamnatin tarayya da ke Gusau jihar Zamfara, inda suka sace dalibai mata masu tarin yawa. Sai dai bayanai sun ce an kubuto wasu daga cikinsu.

Sashen hulda da jama'a na jami'ar ta FUDMA bai kai ga fitar da sanarwa kan lamarin ba a hukumance. Amma dai DCL Hausa ta kira sashen, wani daga cikin ma'aikatan ya ce zai kira idan sun kammala tattara bayanai. 

Rundunar 'yan sandan jihar Katsina ta hannun mai magana da yawun ta ASP Sadiq Aliyu Abubakar ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce an kama mutum daya da ake zargi yana ba 'yan ta'addar bayanan sirri, sannan an kama wasu mutane da dama da ake zargi da hannu a satar wadannan dalibai mata na Jami'ar FUDMA, Katsina. 

Rundunar 'yan sandan ta ce tana ci gaba da gudanar da bincike tare da tsaurara tsaro don ceto daliban da sauran mutane da 'yan ta'adda ke tsare da su.

Post a Comment

Previous Post Next Post