Majalisa ta ja kunnen Tinubu kan kisan kudi ba bisa ka'ida ba

Majalisar dokokin Nijeriya ta ja kunnen shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu kan kashe kudi ba bisa ka'ida ba, har ma ta shawarce shi da ya mika mata kasafin kudin cike gibi na 'supplementary' musamman kan batun iskar gas.

Majalisar ta hannun shugaban kwamitin majalisa dattawa kan iskar gas Sanata Jarigbe Jarigbe ta bukaci sashen zartarwar da ya mika mata kasafin kudin cike gibi na 2023 don fara aikin inganta bangaren iskar gas.

Wannan bukata dai ta zo ne kasa da sa'o'i 48 bayan da shugaban kasa Bola Tinubu ya sanar da daukar matakan saukaka rayuwa bayan cire tallafin man fetur ga 'yan Nijeriya.

'Yan majalisar sun tsaya kai da fata cewa ya kamata a rika kashe kudi a hurumin doka.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp