Gwamnatin Tinubu za ta mayar da yara milyan 10 makarantun boko

Gwamnatin tarayya ta sanar cewa tana nan tana shirin mayar da yara milyan 10 makarantun boko a fadin kasar nan da wasu 'yan shekaru masu zuwa.

Karamin ministan ilmi Dr Yusuf Tanko Sununu ya sanar da hakan a lokacin da ya karbi bakuncin 'yan majalisar dokoki na jam'iyyar APC a Abuja.

Babban jami'in kungiyar 'yan majalisar dokokin wanda shi ne mataimakin shugaban majalisar wakilai Babangida Nguroje bayan taya murna ga ministan, ya bukaci da su saka idanu sosai kan ilmin yara kanana musamman masu karamin karfi.

Sai dai da ya ke mayar da jawabi, Dr Yusuf Sununu ya ce gwamnati na shirin mayar da yara milyan 10 makarantun boko.

Ya ce gwamnati na da burin dasa harsashi mai dorewa a kan ilmi ta hanyar bullo da matakan da za su sa yaran su ji su na son zuwa makarantar ta hanyar samar musu yanayi mai kyau.

Post a Comment

Previous Post Next Post