Gawuna zai sake farfado da kasuwancin da aka rusa a Kano idan aka rantsar da shi - Ganduje

Shugaban jam'iyyar APC na kasa Abdullahi Ganduje ya tabbatar wa da 'yan kasuwar Kano cewa za su dara idan jam'iyyar APC ta dawo mulki a jihar.

Gwamnan jihar Kano na yanzu Engr Abba Kabir Yusuf tun bayan da ya karbi ragamar tafiyar da gwamnatin jihar, ya fara rusa wasu wurare da ya ce an gina su bisa son zuciya.

Duk da Gwamnan ya sha fadin cewa yana wadannan rushe -rushe ne don tsaftace gari da inganta kasuwanci a jihar, amma wasu na ganin cewa yana yin hakan ne don dakushe tarihin ayyukan raya kasa da tsohon Gwamna Ganduje ya yi a jihar.

A ranar 20 ga watan Satumba ne dai kotun sauraren kararrakin zabe ta jihar ta yanke hukuncin cewa jam'iyyar APC ce ta yi nasara a zaben Gwamnan jihar Kano ba NNPP. Sai dai dukkanin jam'iyyun biyu sun garzaya kotun daukaka kara.

Da ya ke karbar matasan 'yan kasuwa na jihar Kano a sakatariyar jam'iyyar APC ta kasa da ke Abuja, Abdullahi Ganduje ya ba su tabbacin cewa jam'iyyar APC idan ta dawo kan mulki za ta maido musu da martaba da kimar kasuwancinsu.

Tsohon Gwamna Ganduje ya ce yanzu mutane da dama na dari-darin zuwa Kano don gudanar da kasuwanci.

Post a Comment

Previous Post Next Post